IQNA

An Kirayi Musulmin Nigeria Da Su Duba Watan Ramadan A Yau

15:44 - August 11, 2010
Lambar Labari: 1970993
Bangaren kasa da kasa; Majalisar koli ta malaman addinin Musulunci ta kasar Nigeria ta kirayi dukkanin musulmin kasar da su zura ido a cikin sararin samaniya a yammacin yau domin ganin watan Ramadan.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar Nigerian Tribune an habarta cewa, majalisar koli ta malaman addinin Musulunci ta kasar Nigeria ta kirayi dukkanin musulmin kasar da su zura ido a cikin sararin samaniya a yammacin yau domin ganin watan Ramadan mai alfarma.

Babban sakataren majalisar kolin malaman addinin muslunci a tarayyar Nigeria malam Abdullatif shi ne ya fitar da wannan sanarwa, da a cikinta aka bayayna cewa dukkanin musulmin Nigeria su duba jinjirin watan Ramadan a yammacin yau talata.

Ya ce bisa ga ka'ida ta muslmin ana fara duba watan Ramadan a ranar 29 ga watan sha'aban, idan an ga wata to rana ta gaba za a dauki azumin Ramadan, idan kuma ba a gan shi ba, sai watan sha'aban ya cika kawanaki talatin cur.

630589



captcha