IQNA

Taron Baje Kolin Littafan Musulunci Na Ramadan A Belgium

15:44 - August 11, 2010
Lambar Labari: 1970995
Bangaren kasa da kasa; Ana shirin fara gudanar da taron baje kolin littafan addinin muslunci da aka saba gudanarwa shekara-shekara a kasar Belgium a duk lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma a birnin Liege na kasar.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Islamic-events na yanar gizo an habarta cewa, ana shirin fara gudanar da taron baje kolin littafan addinin muslunci da aka saba gudanarwa shekara-shekara a kasar Belgium a duk lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma a birnin Liege na kasar ta Belgium.

Bayanin ya ci gaba da cewa a taron baje kolin za a fitar da littafai daban-daban da aka rubuta kan ilmomin addinin muslunci, wadanda aka rubuta da harsuna daban-daban, da kuma wadanda aka tarjama.

Haka nan kuma ana baje kolin wasu daga cikin kayayyakin fasahar Musulunci da suka hada alluna da kuma zane-zane, da aka kayata da adon rubutun larabci.

630453



captcha