Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban cibiyar kula da ayyukan kur'ani mai tsarki ta sayyida Rukayya (AS) ya bayyana cewa, an bude wani sabon shafin yanar gizo da ya kebanci mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar saudiyya makaranta kur'ani mai tsarki a yankunan gabacin kasar Saudiyya da yankunan da ke kusa da su.
Ya ci gaba da cewa bude wannan shafin yanar gizo yana da matukar muhimmanci ga mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke zaune a yankunan gabacin kasar Saudiiya, domin kuwa babu wanda zai hana su amfana da shi.
Mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) da ke gabacin kasar Saudiyya suna fuskantar matsaloli da takurawa daga gwamnatin wahabiyawan saudiyya masu tsananin gaba da bin tafarkin iyalan gidan ma'aiki.
630373