IQNA

Limamin Kirista A Faransa Ya Taya Musulmi Muranar Azumi

12:46 - August 12, 2010
Lambar Labari: 1971971
Bangaren kasa da kasa; Babban malamin majami'ar yankin Velence a kasar Faransa Jean Cristof a cikin wani bayani da ya fitar ya taya dukkanin al'ummar musulmi na kasar Faransa murnar shiga watan Ramadan mai alfarama.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wani shafin yanar gizo eglise an habarta cewa, babban malamin majami'ar yankin Velence a kasar Faransa Jean Cristof a cikin wani bayani da ya fitar ya taya dukkanin al'ummar musulmi na kasar Faransa murnar shiga watan Ramadan mai alfarama da aka shiga.

A cikin bayanin da ya bayyana cewa watan ramadan daya ne daga cikin watanni da suke da matukar muhimmanci ga mabiya addinin musulunci, inda suke gudanar da ayyuka na ibada a cikinsa, ya ce a kan haka yana taya dukkanin musulmin kasar Faransa.

630805










captcha