IQNA

A Yau Ne Za A Bude Agogo Mafi Girma A Duniya A Makka

12:45 - August 12, 2010
Lambar Labari: 1971972
Bangaren kasa da kasa; Za a bude agogo mafi girma a duniya ta farko a birnin Makka mai alfarma a rana ta farko a cikin watan Ramadan mai alfarma, wadda aka gina babban bango da zai dauke ta a kusa da masallacin ka'aba.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar al-ittihad ta buga labarin da ke cewa, z a bude agogo mafi girma a duniya ta farko a birnin Makka mai alfarma a rana ta farko a cikin watan Ramadan mai alfarma, wadda aka gina babban bango da zai dauke ta a kusa da masallacin ka'aba mai alfarma


Rahoton ya ce taron bude wannan makeken agogo ya samu halartar baki daga kasashen ketare musamman ma na musulmi da kuma na larabawa, wadanda suka halarci wurin kaddamar da ita.

Agogon dai wadda tsawonta ya kai mita 40, kuma tsawon ginin da take idan an hada zai mita 400, nauyinta kuma ya kai kimanin kilo gram dubu talatin da shida, za a rika auna lokutan Musulunci da ita.

631156
captcha