Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babbar cibiyar khatmar kur'ani mai tsarki ta duniya ta halarci taron baje kolin kur'ani na kasa da kasa na goma sha bakwai da ake gudanarwa a birnin Tehran tare da fitar da kayayyakin sadarwa na zamani ta hanyar yanar gizo wato internet.
Mai aiko ma kamfanin dillancin labaran iqna daga wurin taron baje kolin ya habarta cewa, kasashe 82 ne ke halartar baje kolin daga nahiyoyin duniya daban-daban, wadanda suka kawo nasu kayayyakin na kur'ani.
Bayanin ya ci gaba da cewa daga bangaren cibiyar khatmar kur'ani ta duniya kamfanoni goma ne suka halarci taron, da suka kawo nasu kayan, da suka hada da littafai da aka rubuta kan fannoni na kur'ani.
Mafi yawan musulmin da suka halarci wannan taron baje kolin kur'ani na kasa da kasa sun fit one daga kasashen musulmi, da kuma kasashen yamacin turai gami da latin Amurka.
632306