Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Islamic-events na yanar gizo an bayyana cewa, cibiyar bunkasa harkokin al'adu da ilmomin addinin musulunci ta kasar Belgium ta fara gudanar da shirye-shirye na musamman da suka dangani azumin watan ramadan mai alfarma.
Daga cikin shirye-shiryen da cibiyar ta fara aiwatarwa har da gudanar da taruka na addini domin fadar da musulmi kan muhimmancin azumin watan Ramadan, da kuma karatun kur'ani gami da jawabai.
Daga ciki akwai wadanda aka baiwa taken watan Ramadan watan safkar kur'ani mai tsarki, sai kuma wani shiri mai suna me muka yi domin isar da sakon Allah, da kuma wani mai take tunani a cikin kur'ani.
632277