Bangaren kasa da kasa; An buga tare da watsa wasiyar karshe ta Imam Ali (AS) a kasar Turkiya a cikin harshen turkanci, wanda shafin sadarwa na tashar talabijin din samanyolu ya dauki nauyin bugawa tare da yawada a cikin shafin yanar gizo.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na samanyoluhaber an bayyana cewa, an buga tare da watsa wasiyar karshe ta Imam Ali (AS) a kasar Turkiya a cikin harshen turkanci, wanda shafin sadarwa na tashar talabijin din samanyolu ya dauki nauyin bugawa tare da yawada a cikin shafin yanar gizo, domin amfanuwar masu magana da harshen turkanci.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan wasiya ta Imam Ali (AS) tana da matukar muhimmanci ga dukkanin al'ummar musulmi su karanta ta, a kan haka ne ma wannan shafi ya dauki nauyin gudanar da wannnan aiki mai matukar muhimmanci.
632260