Bangaren kasa da kasa; Jam'iya mai mulki a kasar Turkiya ta raba wasu kur'anai da aka tarjama a cikin harshen turanci ga jakadun kasashen ketare da ke kasar, a wani taron buda baki da ta kira a daren jiya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani labari daga shafin sadarwa na stargundem cewa, jam'iya mai mulki a kasar Turkiya ta raba wasu kur'anai da aka tarjama a cikin harshen turanci ga jakadun kasashen ketare da ke kasar, a wani taron buda baki da ta kira a daren jiya a birnin Ankara.
Taron buda bakin bangaren kula da hulda da jama'a na jam'iya mai mulki a Turkiya ya kira, ya gayyaci dukkanin jakadun kasashen ketare da ke kasar, wanda ya kuma ya samu halartar ministan harkokin kasar.
632245