IQNA

Zaman Taro Kan Kusanto Da Fahimtar Musulmi A Dakar

9:53 - August 14, 2010
Lambar Labari: 1972598
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro mai taken rayuwar bai daya da fahimtar juna tsaknain dukkanin al'ummar musulmi a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran lesoleil cewa, za a gudanar da wani zaman taro mai taken rayuwar bai daya da fahimtar juna tsaknain dukkanin al'ummar musulmi a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal, wanda cibiar karafa 'yan uwantaka tsakanin musulmi ta shirya gudanarwa.

Wannan cibiya wadda wasu daga cikin musulmin kasar Senegal suka kafa, ta saba gudanar da irin wadannan taruka da ma wasu tarukan na daban, da nufin kara bunkasa dangantaka tsakanin al'ummar musulmi.

Taron zai samu halartar wasu daga cikin masana daga jami'oin kasar gami da malaman addini da kuma wakilan gwamnati, musamamn ma daga ma'aikatar kula da harkokin addini.

632230





captcha