Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran spa a shafinsa na sadarwa an habarta cewa, za a bude wata babbar cibiya ta horar da masu isar da sakon muslunci a kasashen duniya daban-daban a birnin Makka mai alfarma a cikin wannan wata na Ramadan mai albarka da muke ciki.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan cibiya za ta mayar da hanakali wajen horar da masu sha'awar shiga cikin masu isar da sakon Musulunci don kashan kansu a kasashen da suke ko kasashen da suke magana da harshensu.
632218