Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na sabah a shafinsa na yanar gizo an habarta cewa, gidajen talabijin da radiyo na kasar Jamus suna da sanar da loltan buda baki da sahur daidai daidai da lokacin sharia, a sassa daban-daban na kasar, musamman ma a garuruwan da musulmi suke da yawa.
Bayanin ya ci gaba da cewa manufar hakan ita ce fakar da musulmin kasar kan lokutan inbadarsu ta azumin watan Ramadan, wanda kuma kafofin yada labaran Jamus kan yi kokarin dada ma kowane bangare na addini.
Da dama daga cikin musulmin kasar Jamus sun matukar jin dadinsu da hakan, wanda wannan shi ne karo na farko da aka fara samun hakan a kasar ta Jamus.
632194