IQNA

An Shiga Bangaren Karshe Na Gasar Kur'ani A Turkiya

18:32 - August 14, 2010
Lambar Labari: 1973240
Bangaren kasa da kasa; An shuga bangare na karshe a gasar karatu da hardar kur'ani da ake gudanarwa a kasar Turkiya, da ke samun halartar makaranta da mahartadata daga sassa daban-daban na kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Vakit ya habarta a shafinsa na yanar gizo cewa, an shuga bangare na karshe a gasar karatu da hardar kur'ani da ake gudanarwa a kasar Turkiya, da ke samun halartar makaranta da mahartadata daga sassa daban-daban na kasar ta Turkiya.

Wannan gasa dai da aka saba gudanarwa a kowace shekara, tana samun halaratar makaranta ne daga cikin daliban makarantun addinin Musulunci na kasar, da kuma wasu daga cikin makaranta ko mahardata kur'ani da suke da sha'awar shiga.

A kan bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo a lokacin gudanar da gasa, inda akan yi laka'ari da bangaren da makaranci ya fi nuna bajinta zai a bashi kyauta a bangaren.

632157

captcha