IQNA

Shirye-Shiryen Kur'ani Na Cibiyar Sayyida Rukayya (SA)

13:38 - August 15, 2010
Lambar Labari: 1973328
Bangaren kasa da kasa; Cibiyar darul Kur'an ta Sayyida Rukkaya da ke birnin Qom ta fara gudanar da shirye-shiryenta na watan Ramadan mai alfarma da suka shafi kur'ani mai tsarki da aka baiwa take Ruh wa Raihan.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na ruqayya .net an habarta cewa, Cibiyar darul Kur'an ta Sayyida Rukkaya da ke birnin Qom ta fara gudanar da shirye-shiryenta na watan Ramadan mai alfarma da suka shafi kur'ani mai tsarki da aka baiwa take Ruh wa Raihan a cikin birnin na Qom.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan cibiya takan mayar da hanakli wajen shirye taruka da gabatar da jawabai a duk lokacin gudanar da azumin watan Ramadan mai alfar da suka danganci kur'ani.

Bugu da kari kuma cibiyar tana shirya gasar harda da karatun kur'ani da ke samun halartar dalibai daga makarantun addini musamman ma na kur'ani da ke cikin birnin.

632526





captcha