IQNA

Sabuwar Hanyar Tattauanawa Tsakanin Musulmi Ta Tarho A Jamus

13:38 - August 15, 2010
Lambar Labari: 1973329
Bangaren kasa da kasa; An samar da wata sabuwar hanaya ta tattaunawa da shawara tsakanin musulmi da ke kasar Jamus ta hanyar tarho, inda suke bijiro da mas'alolo da suka shafe da kuma tattauna hanyoyin warware su.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an samar da wata sabuwar hanaya ta tattaunawa da shawara tsakanin musulmi da ke kasar Jamus ta hanyar tarho, inda suke bijiro da mas'alolo da suka shafe da kuma tattauna hanyoyin warware sub a tare da samun wata matsala ba.

Rahoton ya ce musulmin kasar Jamus sun lale marhabin da samun wannan sabuwar hanya, domin kuwa ta hakan ne za su iya tambayar masu bayar da fatawowi kan harkokin da suka shafi zamantakewarsu da suke bukatar fatawa.

Duk da cewa kafa wannan sabuwar hanya ya fuskanci matsaloli da dama, amma daga bisani bayan namijin kokarin da wasu kungiyoyin musulmin kasar suka yi ya tabbata.

632498

captcha