IQNA

Karatun Kur'ani Na Bai Daya A Hubbaren Imam Hussain (AS)

13:36 - August 15, 2010
Lambar Labari: 1973330
Bangaren kasa da kasa; mahukuntan birnin Karbala mai alfarma sun sanar da gudanar da wani shiri na karatun kur'ani mai tsarki na bai daya a cikin hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin, inda za a rika karanta juzu'I daya a kowace rana a cikin wannan wata mai alfarma.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na nun ya habarta cewa, mahukuntan birnin Karbala mai alfarma sun sanar da gudanar da wani shiri na karatun kur'ani mai tsarki na bai daya a cikin hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin, inda za a rika karanta juzu'I daya a kowace rana a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan.

Afdal Shami mataimakin gwamnan lardin Karbala ya sheda cewa, wannan shiri cibiyar darul kur'an ce ta kirkiro shi, wadda take da dangantaka da hubbaren Imam Hussain (AS) mai tsarki.

A cikin shirin dai makaranta kur'ani da mahardata daga sassa daban-daban na kasar, musamman ma mazauna birnin mai alfarma, domin su karanta kur'ani a bayyane juzu'I daya a kowace rana.

632636



captcha