IQNA

An Buga Littafin Sadarwa Da Rayuwar Iyali A Mahangar Kur'ani A Labanan

13:37 - August 15, 2010
Lambar Labari: 1973331
Bangaren kasa da kasa; An buga tare da yada littafin sadarwa da rayuwar iyali a mahangar kur'ani mai tsarki a kasar Labanan, wanda marubucin nan dan yankin Katif na kasar Saudiyya Hussain Mustafa ya rubuta.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin kamfanin dillancin labaran kur'ani na muzn an habarta cewa, an buga tare da yada littafin sadarwa da rayuwar iyali a mahangar kur'ani mai tsarki a kasar Labanan, wanda marubucin nan dan yankin Katif na kasar Saudiyya Hussain Mustafa ya rubuta kuma mu'assasar darul baida ta dauki nauyin bugawa.

Bayanin ya ci gaba da cewa littafin ya samu karbuwa a wajen al'ummar kasar Labanan, bisa la'akri da muhimman abubuwan da marubucin ya bijiro da su a cikin littafinsa na ilimi kan rayuwar zamantakewar iyali.

Bayan haka kuma marubucin ya yi amfani da salon a zamani wajen fitar da hanyoyi na ilimi a mahangar kur'ani kan yadda za a yi amfani da kafofin sadarwa domin kyautata rayuwar zamnatakewa bisa mahanga ta Musulunci.

632575


captcha