IQNA

Kasuwar Baje Kolin Littafan Musulunci A kasar Turkiya

13:36 - August 15, 2010
Lambar Labari: 1973332
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani baje kolin littafan addinin muslunci a birnin Istanbul na kasar Turkiya a cikin a watan gobe da zai samu halartar madaba'antun buga littafai daga kasashen musulmi da na larabawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Turkiya an habarta cewa, za a gudanar da wani baje kolin littafan addinin muslunci a birnin Istanbul na kasar Turkiya a cikin a watan gobe da zai samu halartar madaba'antun buga littafai daga kasashen musulmi da na larabawa daban-daban.

Rahoton ya ce wannan na daya daga cikin manyan baje koli da kasar za ta gani, domin kuwa za a kawo littafai da suka shafi dukkanin bangarori na ilimin addinin Musulunci da koyarwar kur'ani.

Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka hukumar kula da bunkasa ayyukan al'adu da ilimin addini ta kasar ta kammla dukkanin shirye-shiryen gudanar da wannan baje koli.

632624




captcha