IQNA

Musulmin Kasar Birtaniya Za Su Gudanar Tarukan Ranar Qods

11:47 - August 16, 2010
Lambar Labari: 1974424
Bangaren kasa da kasa; Mabiya addinin muslunci na kasar Birtania za su gudanar da tarukan ranar Qods da suka hada da gudanar da zanga-zanga a birnin London fadar mulkin juma'ar karshen watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na aimislam na yanar gizo an bayyana cewa, mabiya addinin muslunci na kasar Birtania za su gudanar da tarukan ranar Qods da suka hada da gudanar da zanga-zanga a birnin London fadar mulkin juma'ar karshen watan Ramadan mai alfarma.

Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyar kula da harkokin ahlul bait dake birnin London gami da cibiyar kula da ayyukan muslunci ta kasar ne suka shirya gudanar da tarukan na hadin gwiwa a ranar Qods ta duniya.

Yanzu dubban musulmi gami da kungiyoyin yahudawan da ke kasar masu kiyayya da akidar yahudancin sahyuniya ne suka bayyana shirinsu na shiga wannan zanga-zanga da za a gudanar domin raya ranar Qods.

633724



captcha