IQNA

Ana Raba Kur'anai Da Aka Tarjama Da Harshen Bril A Morocco

11:48 - August 16, 2010
Lambar Labari: 1974425
Bangaren kasa da kasa; Tun daga ranar farko da aka fara gudanar da azumin watan Ramadan aka fara raba kwafin kur'anai da aka tarjama a cikin harshen Bril a masallatan kasar Morocco wanda hukumar kula da ayyukan addini ta kasar ta dauki nauyi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar na muhit an habarta cewa, tun daga ranar farko da aka fara gudanar da azumin watan Ramadan aka fara raba kwafin kur'anai da aka tarjama a cikin harshen Bril a masallatan kasar Morocco wanda hukumar kula da ayyukan addini ta kasar ta dauki nauyin yin hakan.

Ma'ikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar Morocco ta dauki nauyin buga kwafi-kwafi na kur'ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen Bril kimanin dubu satin da biyu domin raba su ga mutane.

Bisa ga al'ada a duk lokacin da aka fara azumin watan Ramadan mai alfarma, muslmin kasar Morocco su kan gudanar da tarukan addini a masallatai da ke garuruwa daban-daban na kasar, da hakan ya hada da karatun kur'ani a daraen watan mai alfarma.

633709




captcha