IQNA

Musulmin Faransa Sun Yi Kira Da A Taimaka Ma Mutanen Pakistan

11:47 - August 16, 2010
Lambar Labari: 1974426
Bangaren kasa da kasa; Babbar kungiyar musulmin kasar Faransa ta yi kira ga daukacin musulmin kasar da su taimaka da duk abin da ya sawaka ga al'ummar kasar Pakistan da ambaliyar ruwa ta yi wa yankan kauna.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran AFP cewa, babbar kungiyar musulmin kasar Faransa ta yi kira ga daukacin musulmin kasar da su taimaka da duk abin da ya sawaka ga al'ummar kasar Pakistan da ambaliyar ruwa ta yi wa yankan kauna a cikin 'yan kawanakin nan.

Bayanin ya ci gaba da cewa, bisa la'akari da cewa wannan lokaci mai albarka, ya kamata al'ummar musulmi da ke cikin kasar Faransa su taimaka ma 'yan uwansu musulmi da ke kasar Pakistan.

Yanzu haka kungiyoyin musulmi da ke da rassa da cibiyoyi a sassan kasar sun bude wurare karbar taimako ga al'ummar kasar Pakistan, inda ake ci gaba da tattara abubuwan da ake bayar da nufin aike wa wadanda abin ya shafa.

633712




captcha