Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na uitm cewa, za a gudanar da wani zaman taro a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia, dangane da yadda ake sanin laifi a tsarin harkokin kudi a mahangar addinin muslunci da zai samu halartar masana.
Cibiyar kula da harkokin kudi ta jami'ar birnin Kualalampour ce za ta dauki nauyin shirya wannan zaman taro da zai samu halar wasu daga cikin manyan malaman jami'ar da suke bangaren lissafi da tattalin arziki.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro na da matukar muhimmanci ga dukkanin musulmi da suke gudanar da harkokin kasuwanci gami da sauran harkokin kudi, domin kuwa zai yi dubi dalla-dalla kan mahangar addinin Musulunci a dukkanin bangarori da suka shafi hakan.
633602