Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga bangaren kula da hulda da jama'a na cibiyar kula da harkokin kur'ani cewa, an aiwatar da gagarumin shirin nan na khatmar kur'ani mai tsarki wanda babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani ta jamhuriyar Musulunci ta bullo da shi tare da mika shi ga bangaren ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasa baki daya.
Ya ci gaba da cewa wannan shiri ya samu karbuwa daga kungiyoyin kur'ani na kasashen musulmi da wasu kasshen larabawa da ma wasu kasshen duniya na daban, inda wakilai daga kashe kimanin tamanin da biyu daga sassan duniya suka yi rijistar shiga cikin shiri.
Cibiyar kula da harkokin kur'ani tare da bunkasa koyarwarsa a duniya da ke da babbn afishinta a jamhuriyar Musulunci tana taka gagarumar rawa wajen wayar da kan al'ummomin duniya dangane da koyarwar kur'ani mai tsarki.
634524