IQNA

An Girmama Wata Karamar Yarinya Bairaniya Da Ta Hardace Kur'ani

10:36 - August 17, 2010
Lambar Labari: 1974938
Bangaren kur'ani; An girmama wata karamar yarinya bairaniya mai suna Rukayya Muhammadi da ya hardace kur'ani mai tsarki tana shekaru takwas da haihuwa a wani taron mahardata kur'ani da aka gudanar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an girmama wata karamar yarinya bairaniya mai suna Rukayya Muhammadi da ya hardace kur'ani mai tsarki tana shekaru takwas da haihuwa a wani taron mahardata kur'ani da aka gudanar a lardin Fars.

Rahoton ya ce yanzu haka dai mahardata kur'ani sama da dubu daya ne gami malaman jami'a suke halartar wannan taro na mahardata kur'ani, inda Rukayya ta gudanar da karatun kur'ani mai tsarki.

Da dama daga cikin malaman jami'a da suka halarci zaman taron daga wasu jami'o na kasashen waje sun nuna matukar mamakinsu dangane da irin baiwar da Allah ya yi wa wannan yarinya.

634592

captcha