IQNA

Za A Harba Tauraroron Dan Adam Domin Ganin Wata A Masar

11:50 - August 17, 2010
Lambar Labari: 1974939
Bangaren kasa da kasa; An kammala shirin harba wani tauraron dan adam domin ganin jinjirin wata a cikin sararin samaniya a kasar Masar, wanda zai fara aiki nan ba da jimawa ba a matsayin gwaji.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, wani rahoto da shafin sadarawa na yanar gizo na Arabic.irib.ir ya bayar an bayyana cewa, an kammala shirin harba wani tauraron dan adam domin ganin jinjirin wata a cikin sararin samaniya a kasar Masar, wanda zai fara aiki nan ba da jimawa ba a matsayin gwaji domin tabbatar da yana aiki kuma babu wata matsala.

Bayanin ya ci gaba da bisa bayanan da jami'an ma'aikatar kula da harkokin sararin samaniya na kasar Masar suka bayar, wannan shirin zai taimaka matuka wajen kawo karshen matsalar ganin watan Ramadan da ake fama da ita.

Hukumar kula da ayyukan harkokin sararin sanaiya ta kasar Masar tare da hadin gwiwa da wata cibiyar sararin samaniya ta kasar Italia ne suke gudanar da aikin hada taroron dan adama din, wanda za a harba nan ba da jimawa ba.

634437


captcha