IQNA

Watan Azumi Dama Ce Ta Tabbatar Da Dokokin Kur'ani

11:37 - August 18, 2010
Lambar Labari: 1976016
Bangaren kasa da kasa; Shaharraren makarancin kur'anin nan na kasar Masar Mahmud Sadiq Manshawi ya bayyana cewa lokacin watan Ramadan dam ace ta tabbatar da dokoki da hukunce-hukuncen kur'ani mai tsarki.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na Mukhtasar ya bayyana cewa, shaharraren makarancin kur'anin nan na kasar Masar Mahmud Sadiq Manshawi ya bayyana cewa lokacin watan Ramadan dama ce ta tabbatar da dokoki da hukunce-hukuncen kur'ani mai tsarki tsakanin al'ummar musulmi.

Bayanin ya ci gaba da cewa, malamin ya jaddada muhimamncin karatun kur'ani a cikin watan Ramadan, inda musulmi za I iya yin amfani da wannan damar domin karfafa tilawarsa da kuma aitar da abin da ya sani dokokin karatun kur'ani.

Ya yi shara da cewa a cikin watan Ramadan ya kan karanta juzu'i goma na kur'ani, duk kuwa da bahasin da yake abangaren tafsiri da sauran ilmo na kur'ani mai tsarki.

635630




captcha