Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kasar Senegal APS an bayyana cewa, a ranar lahadi mai zuwa ce za a fara gudanar da gasar kur'ani ta kasa a karo na goma sha bakawai a kasar Senegal tare da halartar malamai gami da makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki na kasar.
Rahoton babban kwamitin matasa musulmi na kasar Senegal ne tare da hadin gwiwa da kungiyar raya ilmomin addinin Musulunci ta duniya ne ke shirya gudanar da wannan gasa a kowace shekara.
Sama da kungiyoyi da cibiyoyin kur'ani 40 ne daga sassa daban-daban na kasar Senegal kan halarci wannan gasa, inda a kan kasa bangarorin gasar gwargwadon hardar masu halartar gasar, wasu bangare hardar dukkanin kur'ani wasu kuma a bangaren juzu'i- juzu'i.
Shugaban kasar Senegal ne jagoranci bude taron gasar kur'nin, tare da halartar manyan malaman addinin muslunci na kasar, gami da shugabannin cibiyoyin addini daban-daban na kasar.
635333