IQNA

Za A Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Kasa Da Kasa A Dubai

12:13 - August 19, 2010
Lambar Labari: 1976716
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da kasa da kasa a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa, da za ta samu halartar makaranta daga kasashen musulmi.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar khalij an bayyana cewa, za a fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da kasa da kasa a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa, da za ta samu halartar makaranta daga kasashen musulmi da na larabawa.

Bayanin ya ci gaba da cewa a lokacin gudanar da taron bude gasar, sarkin birnin Dubai Muhammad bin Rashid Ali Maktum ne zai jagoranci bukin bude gasar, da za ta samu halartar jami'an gwamnati da malaman addini gami da cibiyoyin kur'ani na kasar.

Yanzu haka dai an kallama dukkanin shirye-shiryen fara gudanar da wannan gasa, inda daruruwan makaranta na kasar da kuma na kasashen duniya suke cikin shiri.

636093










captcha