Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin yanar gizo na jaridar Al-raya ta kasar Qatar cewa, an gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da kebnci jami'an tsaro a kasar Qatar da aka saba gudanarwa a kowace shekara a lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma a birnin Doha fadar mulkin kasar.
Ali Ahmad Barik shugaban kwamitin da ke shirya gudanar da irin wannan gasa a kasar ya bayyana cewa, yanzu haka akwai masu gudanar da gasa har mutum 60 da suke cikin karawa da juna, inda daga karshe za a rika fitar da mutanen da suka yi nasara a rukunoni.
Ya kara da cewa an kasa bangarorin gasar ne zuwa kashi goma daidai da yadda aka yi rijistar sunayen mutane da bangarorin da suka hardace na kur'ani mai tsarki, kamar yadda wasu kuma suka hardace kur'anin baki daya.
636123