IQNA

Za A Bude Bangaren Kasa Da Kasa A Baje Kolin Kur'ani A Tehran

12:09 - August 19, 2010
Lambar Labari: 1976718
Bangaren kasa da kasa; Za a bude bangaren kayayyaki na kasa da kasa a baje kolin kur'ani na duniya da ke gudana a birnin Tehran faar mulkin jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda ake gudanarwa a karo na goma sha bakwai.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da shugaban bangaren kula da harkokin baje kolin kur'ani a Iran Mahdi Mostafavi ya bayyana cewa, za a bude bangaren kayayyaki na kasa da kasa a baje kolin kur'ani na duniya da ke gudana a birnin Tehran faar mulkin jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda ake gudanarwa a karo na goma sha bakwai a kasar.

Ya ci gaba da cewa an fara gudanar da taron baje kolin kur'anin net un a cikin makon da ya gabata, kuma dukkanin kayayyakin da aka baje na cikin gida ne, kuma yanzu haka an kammala dukkanin shirye-shirye na bude bangaren kayayyaki na kasa da kasa.

Cibiyoyin adinin Musulunci da madaba'antu daga kasashen musulmi da na larabawa daban-daban duk sun hallara a baje kolin, inda za su baje irin nasu kayyakin na rubuce-rubuce da suka danganci kur'ani mai tsarki.

636189






captcha