IQNA

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi Ta Bukaci A Taimakawa Pakistan

12:11 - August 19, 2010
Lambar Labari: 1976801
Bangaren kasa da kasa; Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya fitar da wani bayani da a cikinsa ya bukaci da a agazawa Pakistan cikin gaggauwa kuma ya bukaci hakan ne ga kasashen musulmi mambobi a kungiyar.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci na Iran bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta haberoku ta watsa rahoton cewa; Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya fitar da wani bayani da a cikinsa ya bukaci da a agazawa Pakistan cikin gaggauwa kuma ya bukaci hakan ne ga kasashen musulmi mambobi a kungiyar. Ya zo a cikin sanarwar cewa yawan kudaden da kungiyoyin kasa da kasa suka ware ya kasa kuma na shigowa ne a hankali cikin lati saboda haka ana bukatar taimakawa mutanen da lamarin ya shafa cikin gaggauwa ba tare da bata lokaci bat un kafin matsalar ambaliyar ruwa ta yi kamari da kara yawa.


636347


captcha