IQNA

An Bude Masallaci Da Cibiyar Musulunci A Kasar Tanzania

11:17 - August 22, 2010
Lambar Labari: 1977316
Bangaren kasa da kasa; An bude wata makarantar addinin Musulunci da ke hade da wani babban masallci gami da cibiyar ayyukan Musulunci a tsibirin Zanjibar na kasar Tanzania.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran haber an bayyana cewa, an bude wata makarantar addinin Musulunci da ke hade da wani babban masallci gami da cibiyar ayyukan Musulunci a tsibirin Zanjibar na kasar Tanzania dake gabacin nahiyar Afirka.

Rahoton ya ce wannan makaranta dake hade da masallaci gami da babbar cibiyar kula da ayyukan Musulunci an gina su domin amfanin musulmin tsibirin Zanjibar da kuma na kasar Tanzania baki daya.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta IHH ta kasar Turkiya ce ta dauki nauyin gina wannan makaranta, an kuma gudanar da bukin budewa tare da halartar firaministan tsibirin Zanjibar.

637400












captcha