IQNA

Taro Kan Kur'ani A Yankin Ihsa Na Kasar Saudiyya

11:19 - August 22, 2010
Lambar Labari: 1977317
Bangaren kasa da kasa; Babbar cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta dar al-rahman a lardin Ihsa na ka sara Saudiyya za ta gudanar da wani zaman taro kan bahasin ma'anonin ayoyin kur'ani da aiki da su a cikin rayuwar zamantakewa.


Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya nakalto daga shafin tashar sadarwa ta rasid cewa, babbar cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta dar al-rahman a lardin Ihsa na ka sara Saudiyya za ta gudanar da wani zaman taro kan bahasin ma'anonin ayoyin kur'ani da aiki da su a cikin rayuwar zamantakewar al'ummar musulmi.

Wannan taro shi ne irinsa karo na bakwai da za a gudanar a lardin Ihsa wanda cibiyar ta dar al-rahman ta kan shirya tare da gudanarwa a cikin kowane watan azumin Ramadan, kamar yadda aka yi shekaru shida da suka gabata.

Daga cikin abubuwan da ake gudanarwa a yayin taron har da gabatar da laccoci daga malamai daban-daban, kamar yadda akan gabatar da makaloli da aka rubuta kan maudu'ai na kur'ani mai tsarki a bangarori daban-daban.

637398

captcha