IQNA

An Buga Littafin Al'adu Da Demokradiya A Duniyar Musulunci

11:17 - August 22, 2010
Lambar Labari: 1977318
Bangaren kasa da kasa; An buga wani littafi mai suna na'in al'adu da demokradiya a duniyar musulmi a cikin harshen faransanci wanda wata cibiyar bunkasa harkokin al'adu da ilimi ta kasar Morcco ta dauki nauyin bugawa.


Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar Al'alam ta kasar Morocco an habarat cewa, an buga wani littafi mai suna na'in al'adu da demokradiya a duniyar musulmi a cikin harshen faransanci wanda wata cibiyar bunkasa harkokin al'adu da ilimi ta kasar Morcco ta dauki nauyin bugawa tare da rabawa a sassa daban-daban na duniya.

A cikin rahoton ya cewa, wannan littafi ya yi bahasi kan rawar da al'adu suke takawa acikin rayuwar jama'a ta zamantakewa a cikin kasashen musulmi, tare da matsayin demokradiya a mahangarsu a wannan zamani da kuma yadda ake yin aiki da ita a cikin wadannan kasashe.

Littafin ya hada jawabai da dama dam asana suka yi, gami da makaloli da aka rubuta a jami'oin kasar kan matsayin demokradiya da mahangar al'ummomin muulmi kanta, da kuma yadda hakan ke tasiri a cikin rayuwar zamantakewarsu.

637395







captcha