Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani bayani daga shafin sadarwa na yanar gizo batiweb cewa, za a gudanar da wani baje kolin kayayyakin fasahar Musulunci a nahiyar turai a cikin wata mai kamawa a birnin Paris na kasar Faransa, wanda wata cibiyar kula da harkokin al'adun muslunci za ta gudanar a birnin na paris.
Daga cikin muhimman abubuwan da za a nuna awajen wannan baje koli har da kayyakin gini da aka yi amfani da su wajen tsara wasu wurare masu tsarki a cikin addinin Musulunci, gami da hotuna na ayyukan da musulmin ke gudanarwa akasashen nanhiyar turai.
637375