Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran kur'ani na muzn ya habarta a shafinsa na sadarwa na yanar gizo cewa, tashar talabijin din kasar Bahrain ta goma sha hudu 14 za ta fara gudanar da wani shiri na kur'ani mai tsarki saboda raya ranakun watan Ramadan mai alfarma ga al'ummar kasar.
Rahoton ya ce wannan shiri zai mayar da hankali ne kan muhimman abubuwan da ya kamata musulmi ya mayar da hanakali kansu a cikin watan Ramadan mai alfarma, domin samun falalar watan da kuma ayyukan ibada da ake gudanarwa a cikinsa.
Daga cikin shirye-shiryen har da jawaban malamai kan ayoyin kur'ani mai tsarki da suke magana kan tarbiyar dan adam da kuma lizimtar dokokin ubangiji a cikin rayuwa.
637366