Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na acikgateze na yanar gizo cewa, za a bude wata jami'ar Musulunci wadda ita irinta ta farko a kasar Amurka a kusa da jami'ar Barcly da ke cikin jahar California ta kasar Amurka.
Daya daga cikin malaman jami'a a kasar ta Amurka, kuma mabiyin addinin Musulunci Rida Aslan ya bayyana cewa za a koyar da ilmomi na addinin muslunci da kuma sauran ilmomin book a wannan jami'a.
Yanzu ahka dai mahukuntan kasar Amurka ajahar California sun bayar da izinin gina jami'ar tare da sa hannun sauran cibiyoyin ilmi na jahar da kuma cibiyoyin Musulunci.
637601