IQNA

Gasar Hardar Kur'ani Mai Tsarki Ta Kasa A Kuwait

13:56 - August 24, 2010
Lambar Labari: 1980323
Bangaren kasa da kasa; Babban daraktan kwamitin kula da harkokin addini da na zamantakewar jama'a akasar Kuwait Salih Al-auda ya sheda cewa za a gudanar da gasar hardar kur'ani mia ta kasa a kasar Kuwait.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar kasar Kuwait Al-ray a habarta cewa, babban daraktan kwamitin kula da harkokin addini da na zamantakewar jama'a akasar Kuwait Salih Al-auda ya sheda cewa za a gudanar da gasar hardar kur'ani mia ta kasa a kasar Kuwait mai suna Al-kasaf.

Rahoton ya ce bisa bayanin da babban daraktan ya bayar, gasar za ta samu halartar mahardata daga sassa daban-daban na kasar, inda za su kar ada juna abangarorin da aka zayyana cewa gasar za ta mayar da hankali a kansu.

Daga cikin tsarin gasar za a banbanta yanayin zurfin hardar dukkanin masu halartar gasar, inda wasu za su fara daga bangaren farko zuwa tsakiya, wasu za su yi a dukkanin bangarori na kur'ani.

639722



captcha