IQNA

Ci Gaba Da Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Duniya A Dubai

13:56 - August 24, 2010
Lambar Labari: 1980326
Bangaren kasa da kasa; Ana ci gaba da gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa, inda makaranta bakwai suka yi saura daga kasashen daban-daban.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar kula da harkokin gasar kur'ani ta Dubai an bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa, inda makaranta bakwai suka yi saura daga kasashen daban-daban da suka hada da Birtaniya, Tunisi, Oman, Auzbakistan, Aljeria, tsibirin Komor da kuma Gambia.

Duukkanin akarantan bakwai suna karawa da juna ne a mataki na kusa da na karshe, domin fitar da wadanda za su kara da juna a mataki na karshe, ta yadda za a fitar da na daya da na biyu da kuma na uku.

639541



captcha