Bangaren al'adu da fasaha; Fim din annabi Yusuf (AS) ya samu gagarumar karbuwa a wajen akasarin musulmin kasar Azarbaijan, inda akan saka shi a gidajen talabijin din kasar a lokutan da ake gudanar da shan ruwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar kula da bunkasa harkokin addinin Musulunci da al'adu ta Iran cewa, fim din annabi Yusuf (AS) ya samu gagarumar karbuwa a wajen akasarin musulmin kasar Azarbaijan, inda akan saka shi a gidajen talabijin din kasar a lokutan da ake gudanar da shan ruwa a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa musulmin kasar Azarbaijan suna bayar da muhimmanci ga fina-finan da ake shiryawa na addinin Musulunci, amma a wannan karon sun bayar da muhimmanci na musamman ga fim din annabi Yusuf.
Rahoton ya kara da cewa fim din da aka shirya kan annabi Yusuf (AS) a jamhuriyar musulnci ta Iran ya ginu a kan nassosi na tarihi da dukkanin bangarorin musulmi suka hadu a akan ingancinsu.
639775