IQNA

A Karon Farko Musulmi Ya Zama Dan Majalisa A Austria

15:13 - August 25, 2010
Lambar Labari: 1981226
Bangaren kasa da kasa; Ed Husic bayan ya samu kuri'u mafi yawa da rinjaye a zaben yan majalisa na yankin da ya tsaya ya zama dan majalisar dokoki a kasar ta Austria.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga webhaber ya watsa rahoton cewa; Ed Husic bayan ya samu kuri'u mafi yawa da rinjaye a zaben yan majalisa na yankin da ya tsaya ya zama dan majalisar dokoki a kasar ta Austria. Shi dai wannan musulmi ya kasance mamba a kungiyar ma'aikatan kwadago na Austria kuma musulmi dan asalin kasar Bosniya da ke zaune a kasar kuma yawan kuri'un day a samu ne ya ba shi damar zama dan majalisar dokoki a kasar ta ostriya.Ya zuwa wannan karo babu wani musulmi a wannan kasa day a yi sa'ar zama dan majalisa wannan shi ne karon farko a tarihin kasar.

640603
captcha