Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran sondakika an bayyana cewa, an gudanar da bangaren karshe na gasar hardar kur'ani mai tsarki a kasar Turkiya, wanda shi ne karo na bakwai da ake gudanar da irin wannan gasa a kasar a kowace shekara daga cikin shekarun da suka gabata.
Ali Melek babban malami mai bayar da fatawa a garin Diyar Bakr ya bayyana cewa, an gudanar da wannan gasar ne bisa himmar da cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasar ta nuna, tare sauran cibiyoyin addini na kasar.
Ya kara da cewa mahardata da makaranta kur'ani mai tsarki daga sassa daban-daban na kasar ne suka halarci gasar gasar, kuma tuni aka kammala bangaren karshe.
640343