Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na musulmin kasar kasar Austria an habarta cewa, Babbar cibiyar addinin Musulunci ta birnin Vienna na kasar Austria mai suna cibiyar Imam Ali (AS) tana shirin gudanar da wani gagarumin taron maulidin Imam Hassan Al-mojtaba (AS) da zai samu halartar musulmi daga bangarori daban-daban na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin shirye-shiryen gudanar da wannan taro sun kammala, kuma a daren yau ne za a gudanar da taron, inda za a fara da karatun kur'ani mai tsarki, a tsakanin lokacn sallolin magarib da Isha.
Daga bisani kuma bayan kammala sallo baki daya tare da buda baki, za a saurari bayanai daga malaman da za su halarci taron, kan tarihin rayuwar Imam Hassan Mojtaba (AS) da kuma darussa daga rayuwarsa mai tsarki
640334