IQNA

Muhimmancin Kyuatatar Dangantakar Yammaci Da Musulmi

13:34 - August 26, 2010
Lambar Labari: 1981706
Bangaren kasa da kasa; Babban sakataren kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi Abdula'ziz Tuwaijari ya bayyana cewa, kyautatar lamurra a duniya na da dangataka da kyautatuwar lamurra tsakanin yammacin turai da kuma duniya musulmi.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na Iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na isesco.org.ma an habarta cewa, babban sakataren kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi Abdula'ziz Tuwaijari ya bayyana cewa, kyautatar lamurra a duniya na da dangataka ne kai tsaye da kyautatuwar lamurra tsakanin kasashen yammacin turai da kuma duniyar musulunci.

Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la'akari da irin takun saka da ake samu tsakanin kasashen yammacin turai da kuma musulmi sakamakon siyasar da kasashen turai suke bi wajen nuna kiyayya ga musulmi, dole a kawo karshen hakan matukar dai ana bukatar ci gaba a duniya.

Malamin ya ce dukkanin bangarorin biyu kowane na da matsayi na musamman a duniya, a kan haka babu dalilin da zai sanya musulmi ya zama abin kyama a wajen al'ummomin nahiyar turai.

641235




captcha