Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar darul khalij cewa, an shiga rana ta shiga a gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Dubai, bababr cibiyar harkokin kasuwanci da tattalin arziki ta kasar haddadiyar daular larabawa, wadda a kafa fara a cikin makon da ya gabata.
Rahoton ya ci gaba da cewa yanzu haka dai wadanda suka yi saura daga makaranta da mahardata da ke hartar gasar akwai wakilai daga kasashen Cameron, Yemen, amurka, Rasha, Zambia da kuma Morocco.
Mafi yawan masu gudanar da irin wannan gas adaga kasar nahiyar Afirka musamman daga kasashen Morocco, suna gudanar da gasar ne a cikin kira'ar warshiyya.
641305