IQNA

Taro Kan Matsalolin Zamani Da Hanyoyin Warware Su A Musulunci

15:37 - August 26, 2010
Lambar Labari: 1981750
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro a kasar Turkiya dangane da matsalolin zamanin da muke ciki, da kuma hanyoyin warware su a mahanga ta Musulunci, wanda cibiyar harkokin al'adu ta Istanbul ta dauki nauyin shiryawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na timeturk an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro a kasar Turkiya dangane da matsalolin zamanin da muke ciki, da kuma hanyoyin warware su a mahanga ta addinin Musulunci, wanda cibiyar kula da harkokin al'adu ta birnin Istanbul ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Taron zai samu halartar masana da suka hada da marubuta da malaman jami'a daga sassa daban-daban na kasar gami da kasashen ketare, inda za a gabatar da jawabai da makaloli kan matsayin addinin Musulunci dangane lamurra da daman a rayuwa da kuma zamantakewa, da hanyoyin warware matsaloli.

Daga cikin wadanda za su halarci taro har da babban malamin jami'ar nan ta Cambriege a kasar Birtaniya farfesa Abdulhakim Murad, gami da wasu daga cikin malaman jami'ar.

641515



captcha