Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babbar cibiyar addinai ta kasar Turkiya ta tura wakilanta zuwa babban baje kolin kur'ani na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar Musulunci, wanda hakan ke tabbatar da hadin kai da fahimatar juna ta fuskar addini tsakanin kasashen Iran da Turkiya.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da shugaban tawagar ya bayyana cewa, ko shakka babu zuwansu wannan babban baje kolin kur'ani na duniya a birnin Tehran yana tattare da sakonni masu dama.
Daga cikin irin sakonnin da hakan ke dauke da su har da tabbatar wa duniya cewa akwai kyakkyawar fahimtar juna tsakanin kasashen biyu wato Turkiya da Iran ta fuskoki da dama, da hakan ya hada da fuskar addini.
641359