IQNA

Karatun Kur'ani Mai Tsaki Na Bai Daya A Garin Al-Awamah

15:38 - August 26, 2010
Lambar Labari: 1981753
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da taron karatun kur'ani mai tsarki a garin awamah na kasar Saudiyya, na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah wanda zai samu halar makaranta daga daga bangarori daban-daban na yankin.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar rasid cewa, za a gudanar da taron karatun kur'ani mai tsarki a garin awamah na kasar Saudiyya, na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah wanda zai samu halar makaranta daga daga bangarori daban-daban na yankin da ke gabacin kasar Saudiyya.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taron na daya daga cikin tarukan da aka saba gudanarwa ayankin domin raya dararen watan Ramadan mai alafarma a yankin, ta yadda hakan ya zama daga cikin ayyukan da aka saba da su a kowace shekara.

Daga cikin masu halartar taron har manyan shugabannin kabilun larabawa mabiya mazhabar iyalan gidan manzon da ke cikin yankunan gabacin Saudiyya, kuma an fara gudanar da irin wannan taro net un kimanin shekaru 18 da suka gabata.

641523





captcha