IQNA

Taro A Kasar Turkiya Kan Cika Shekaru 1400 Da Safkar Kur'ani

12:01 - August 28, 2010
Lambar Labari: 1982512
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan cika shekaru 1400 da safkar wahayin kur'ani mai tsarki, wanda cibiyar kula da harkokin al'adu da tarihi ta kasar Turkiya ta shirya gudanarwa.



Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na zaman na yanar gizo an habarta cewa, z a gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan cika shekaru 1400 da safkar wahayin kur'ani mai tsarki, wanda cibiyar kula da harkokin al'adu da tarihi ta kasar Turkiya ta shirya gudanarwa a cikin mako mai zuwa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da suka hada malaman addini, da kuma malaman jami'a gami da masu nazari a bangarori na al'adu da tarihin Musulunci.

Daga cikin wadanda za su halarci taron daga ketare kuwa har da wakilan kungiyoyin musulmi da na al'adu a kasashen musulmi kimanin arba'in, da kuma wasu kasashe da na musulmi ba.

642520

captcha