IQNA

Taron Hukumar Agaji Ta Musulmi A Pakistan

13:18 - August 28, 2010
Lambar Labari: 1982642
Bangaren kasa da kasa; a kasar Pakistan ne hukumomin agaji na kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi za su gudanar da taronsu a ranar lahadi bakwai ga watan Shahrivar a shekarar nan da muke ciki a birnin Islam Abad fadar mulkin kasar Pakistan.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ta nakalto daga majiyar milliyet ta watsa rahoton cewa; a kasar Pakistan ne hukumomin agaji na kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi za su gudanar da taronsu a ranar lahadi bakwai ga watan Shahrivar a shekarar nan da muke ciki a birnin Islam Abad fadar mulkin kasar Pakistan. A wannan taro za a samu halartar Ikmalul dine Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi da kuma Rida Gilani firaministan kasar ta Pakistan da kuma mambobin wannan hukumar agaji ta musulmi da zummar binciken halin da musulmi ke ciki a kasar ta Pakistan da kuma hanyoyin agaza masu.

642401


captcha